Labaran Yau

Obaseki Ya Rage Kwanakin Zuwa Makaranta A Jihar Edo

Obaseki ya rage kwanakin zuwa Makaranta a jihar Edo

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya rage kwanakin zuwa Makaranta na yaran Firamare da sakandare zuwa JSS3 na yara zuwa kwana uku.

Ciyaman na Hukumar kula da ilimin Firamare SUBEB, 0zavize Salami, Ta bayyana wa yan manema labarai bayan zaman da sukayi da Jiga jigen hukumomi kan Umarnin da gwamnati ta bayar na aikin kwana Uku.

Tace sabuwar dokar zata fara aiki daga 13 ga watan Yuni.

Malama Salami tace litinin, talata da laraba aka zaba wajen Makarantar yaran mu, za a kulle Makarantar Alhamis da Jumma’a.

Mun kara lokacin karatu na Firamare a cikin jihar, da awa daya da Kuma awa biyu wa sakandare jss1 zuwa JSS3. Dan samun kammala manhaja Kuma an kara jadawalin karatu na Alhamis da Jumma’a zuwa Litinin, Talata da laraba.”

Shugaban Ma’aikatan jiha, Anthony Okungbowa Yace rage kwanakin aiki ba zai rage aikin da akeyi ko ya kawo rashin aiki ba.

Ya bayyana wa shugabannin hukumomi da ministiri da suyi kokarin gyara jadawali yayi daidai da yanda za a iya cika aiki Kuma su tabbatar babu wani abinda zai kawo cikas a aikin gwamnati.

Ya ce gwamnati zata bada motar bus daga gidan gwamnati, sakateriyan jiha, da da sauransu wajen rage wahala wa mutanen jiha.

Gwamnati ta hango hanyoyi takwas da zata saka mototi dan taimako wa mutane a lokacin tashin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button