Buhari ya kammala tashar wutar zungeru
Gwamnan jihar nega Abubakar Bello ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu buhari wajen kammala gina tashar wutan lantarki wanda ke bada mega watts dari bakwai a zungeru na jihar neja.
Bello yayi yabon ne tare da ministan wuta Abubakar Aliyu, da Shugaban kwamitin wuta na Majalisan dattawa Gabriel suswam, yayin da suka ziyarci tashar wutan zungeru dan gani wa idon su ranar jumma’a.
Yace ita tashar wutan latarkin itace ta hudu a jihar, kuma amfane mutanen jihar yayin da zai bada wutan latarki mai yawa a jihar gaba daya da na waje.
“Zamu samu wuta sosai, aikin tashar wutan zai kawo silar cigaba da dama wajen samun albarkatu ta fanin horaswa, da daman samun aiki” a cewar sa.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar zatayi kokari dan kare wuraren da akayi aikin da tashar wutan a na fadin jihar.
Ya ce aikin ya kai kashi 99 cikin dari na kammala wa, Kuma ya kai a kaddamar da ita.
“Mun saka shugabannin gargajiya su zama idanuwan mu tsakanin gwamnati da mutanen wuraren da akayi aiki.
“Bayan Mun ci gaba, na yarda da daman da zata zo ta haryar noman rani, kasuwanci Duk zasu samu a wannan wuraren” a cewar sa.
A kalaman sa, ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu buhari na yin aikin tashar wutan lantarkin zungeru, saboda a karkashin sa akayi aikin da tun shekarar 1960 ba ayi irin ta ba.
“Mun gamsu da abin da muka gani a nan. kuma ya kamata a ci gaba da sasantawa ba tare da tsangwama ba domin kuwa yan Najeriya su samu moriyar kudaden da aka kashe a kan aikin.
“Mun fi damuwa da layin tura wutar, amma mun ga cewa an hada KV 330 a nan kuma an kusa kammala KV 132, wanda ke nufin cewa yarjejeniyar ta yi kyau kamar yarjejeniyar da aka yi, kuma mun gamsu da hakan,” cewar sa.
Sanata Gabriel Suswam ya kara da cewa a halin da ake ciki, a shirye yake don kaddamar da aikin saboda an gyara dukkan sashin dam din.
Tashar wutar lantarki ta Zungeru mai tsayin mita 95 kuma yana kan kogin Kaduna, ita ce madatsar ruwa ta farko da aka fara amfani da fasahar Roller Compacted Concrete (RCC). Hudu daga cikin injinan an kammala su, kowanne yana da MGW 175 da magudanar ruwa guda hudu dan bada wuta.
Daily Nigeria ta rawaito