Labaran YauNEWSTrending Updates

Speaker House Of Reps Yayi Babban Alkawari Wa Matasa A Zaman Samun Sulhu – 1st August

A majalisar Town hall da aka gudanar a ranar 31 ga watan Yuli, kungiyoyin matasa, sun samu daman tattaunawa a fili tare da cimma matsaya mai inganci da samun alkawarin gwamnati daga kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abass.

An kalli taron majalisar matasan a matsayin wani hanya na yunkurin karshe dan dakatar da hana zanga-zangar da kuma samun fahimtar juna.

Alkawarin Gwamnati Ga Matasa

Shugaban majalisar ya tabbatar da sadaukarwar gwamnati na magance matsalolinsu tare da bayyana shirye-shiryen da ke gudana da kuma masu zuwa da aka tsara don inganta yanayin zamantakewa da tattalin arzikin matasa, in ji PM News.

Shugaban majalisar ya kuma yi alkawarin bayar da kujeru hudu na manyan hadiman majalisa ga kungiyoyin matasa daban-daban domin su zama hanyar sada zumunta tsakanin majalisar da matasan Najeriya a kokarin samar da hanyoyin sadarwa tsakanin bangarorin siyasa da matasa.

Abbas ya ce:

“Wannan gwamnati ta san irin rawar da matasanmu suke takawa wajen tsara makomar al’ummarmu. “Kuma gwamnati ta himmatu wajen samar da yanayin da ake jin muryoyinsu, da kuma daraja gudumawar da suke bayarwa.”

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button