Labaran Yau

Bayan Dogon Bincike, Ta Bayyana Ta Siyar Da Yarinyar Ma Wani A Kudi

An siyar da jariri wata sha takwas a dubu dari shida cewar yan sanda

Yan sanda a jihar ogun sun kama wata mata mai shakara 33 a duniya wanda aka zargeta da siyar da jaririn wata goma sha takwas a farashin dubu dari shida a yankin sango ota a jihar ogun .

Labarin ta samo kanta a jawabin da yan sanda suka sanar a sango ota ran Monday daga bakin supritandan dan sanda Abimbola Oyeyemi, wanda keh magana da yawun yan sandan jiha.

Duk da dai yan sandan basu gano wanda zai siyan ba , an gaggauta kulle wanda ake zargin mai siyarwan a babban ofishin yan sandan sango ota daga hannun mijin ita Mai laifin da ake Tuguma, Nureni Rasaq.

Rasaq ya bayyana cewa

“matarshi ta tafi legas ran sha biyar ga watan maris da yarsu wanda ta dawo babu Yar.

Yayi Duk abinda zaiyi dan ta fadi takamamman Mai ya faru Kuma da Kuma inda Yar take ta kasa fadin komai.

Oyeyemi yace bayan shigar da karan, jagoran ofishin ya bada oda wa CSP Dahiru Saleh da yasa a kama ta. Kuma aka kamata.

Bayan dogon bincike, ta bayyana ta siyar da yarinyar ma wani a kudi duba dari shida a legas.

Ya kara da cewa ta siyar da yarinyan ne dan tabiya bashin da ake binta wanda ta ciyo a bankin Microfinance bisa hakan Ma’aikacin ya razana ta takai da tafiya legas dan neman kudi har ta hadu da wani ya hada ta da wanda zata siyar wa yarinyan.

Mai ruqon kwarya na kujerar kwamishina, DCP Babakura Muhammed wanda yasa aka canza mata guri zuwa zuwa CID dan karin bikcike

Daily Nigeria Ta Rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button