Spokeperson na Senate, Yemi Adaramodu ya tabbatar da mutuwan Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar Anambra ta Kudu a majalisar dattawa. Sanata Uba ya rasu ne a safiyar ranar Asabar 27 ga watan Yuli.
Sanata Ubah, wanda kwanan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ya rasu ne a wani otel dake birnin Landan kwanaki biyu bayan ya bar Najeriya.
Ubah, wanda ya tsaya takarar gwamna a jihar Anambra a shekarar 2014 a karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), ya rasu yana da shekaru 52 a duniya, sakamakon bugun zuciya.
Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Man Fetur a Downstream ya je Landan don halartar bikin yaye dansa.
Shugaban Kasa Tinubu Ya Mika Sakon Ta’aziyyan Late Sen. Ifeanyi Ubah
Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah. Ya kasance shahararren dan kasuwa kuma dan takarar gwamna a zaben gwamnan jihar Anambra da ke tafe.
Da yake mayar da martani kan lamarin, shugaba Tinubu a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Chief Ajuri Ngelale ya fitar, ya yi addu’ar Allah ya kara wa iyalan mamacin karfin gwiwa.
Kalamai Daga Bakin Spokesperson Na Tinubu
Chief Ajuri, yace:-
“Shugaba Tinubu ya jajanta wa abokai da abokan aikin marigayi Sanata, Majalisar Dokoki ta kasa, da gwamnati da al’ummar Jihar Anambra kan wannan babban rashi.
“Shugaban ya yi addu’ar Allah ya hutar da ran dan majalisar da ya rasu, tare da baiwa iyalansa karfin gwiwa da ta’aziyya,” in ji shi.