Chelsea ta amince da yarjejeniyar sayen golan Villarreal Filip Jorgensen da dan wasan bayan Boca Juniors Aaron Anselmino.
Jorgensen, mai shekaru 22, an shirya don duba lafiyarsa bayan an amince da biyan fam miliyan €20.7 kuma ana sa ran ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru bakwai har zuwa 2031.
Dan wasan na Denmark na kasa da shekara 21 ya kasance babban burin sabon koci Enzo Maresca, wanda ke son karin golan da zai iya amfani da kwallon da kyau da kafafunsa.
Jorgensen zai fafata ne da zama na daya a kungiyar, amma yunkurin nasa ya sanya makomar Djordje Petrovic cikin shakku bayan mai tsaron ragar Serbia ya cike gurbin da Robert Sanchez ya samu a kakar wasan da ta wuce a matsayin zabi na farko.
Filip Jorgensen(Goalkeeper) & Aaron Anselmino Sabbin ‘Yan Wasan Da Chelsea Ta Yarda Ta Siya