A gobe ne za a bayyana dan wasan baya Guido Rodriguez a matsayin dan wasan West Ham United, kamar yadda Fabrizio Romano ya fada.
Dan wasan na Argentina zai koma ne a kyauta bayan kwantiraginsa na Real Betis ya kare a farkon bazarar nan.
Rodriguez, mai shekaru 30, ya buga wa Argentina wasa sau 30 tun shekarar 2017 kuma yana cikin gasar cin kofin Copa America da kasar ta yi a watan jiya.
West Ham United a baya ta sanar da daukar dan wasan gaban Jamus Niclas Füllkrug a hukumance. Dan wasan na Jamus ya koma Hammers ne daga Borussia Dortmund kan kwantiragin shekaru hudu kan kudin da ba a bayyana ba.
“Na yi farin cikin kasancewa a nan, kuma ba zan iya jira na fita filin wasa tare da sababbin abokan wasana ba,” in ji Füllkrug.
“Ina ganin gasar firimiya ita ce gasar da ta fi kowacce kyau a duniya, kuma a gare ni lokaci ya yi da zan koma Ingila da taka leda a babbar kulob kamar West Ham.”