Laifina Guda a shugabancin NPA shine rashin bada kyauta na zagayowan haihuwar Ameachi, Hadiza Bala Usman ta bayyana a sabon littafin ta
Manajan darakta wanda aka dakatar Na Hukumar kula da shiga da fitan kaya ta ruwa(Nigeria Port Authority), Hadiza Bala Usman ta fadi dalili guda wanda yasa ministan sufuri, Rotimi Ameachi, ya koreta shine dan ta hana shi kyautan zagayowar haihuwansa.
Ta bayyana hakan a sabuwa littafinta da ta rubuta Kuma ta sake ran talata meh Suna “Stepping on toes” ma’ana “taka yatsun kafa”, labarinta a matsayinta na shugaban tashar jiragen ruwa na Najeriya.
Usman ta kara da cewa jiga jigen gwamnatin sun same shi don sulhuntasu amma abin ya gagara, harda su Shugaban customs Hamid Ali, gwamnan kebbi, Bagudu sunyi kokari dan a dawo da ita, ta rubuta a littafin.
“Kwamitin gwamnoni sun hadu da ministan dan sulhuntawa. Amma ya jajirce akan cewa Suna bincike akan ita hukumar na ta dan kudaden da bata bada ba, yake fadawa gwamnonin cewa kasafin kudi na hukumar yafi karfin kasafin jihohinsu, dan haka karsu damu.
“Bayan gwamnonin sun dage kan Al’amarin, shi minista ya bayyana cewa maganan yafi karfinsa dan Sai sun bai ta kafan Head of service na kasa.
“Ya kara fadi wa wani cewa yaso yayi wani abu akai amma kuma tanada son kanta, yasa taki ta bashi kyauta ran murnan zagayowar haihuwansa.
“Kwantrolan customs ta kasa, Hameed Ali yayi kokari dan yin wani abu akan maganan amma abin yaqi yiwu wa”
A littafin na ta, ta bayyana cewa ba tuntube ta akan Duk abinda ake Zarginta dashi ba, Kuma tayi bakin kokarinta Duk da sanya manyan yan siyasa ciki dan a dawo da ita kujerar ta da aka cire ta, a dalilin babu laifi koh daya.
Dailynigeria ta rawaito cewa a littafin ta tayi duka wannan maganganu.