Labaran Yau

Peter Obi Zai Amsa Tambayoyi Cewar Gwamnatin Tarayya

Obi zai amsa tambayoyi cewar gwamnatin tarayya

Gwammatin Tarayya tace dan takarar shugaban kasa a jam’iyar kwadigo wato Labour Party, Peter Obi, yana da tambayoyiin da zai amsa kan wayarsa da yayi da bisho David Adeboye wanda ta bayyana.

Bayan kwanaki beyi magana ba da fitar sirrin wayar, ya fito ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana baza karyaki akansa, kuma wayar da ta bayyana karyace.

A garin landan dake burtaniya, ministan bayani da Al’ada, Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana wa manema labarai cewa Peter Obi ya musu bayanin wayarsa da Bisho karya ne bayan karyatawa da yayi.

DOWNLOAD MP3

“Inaso in jawo hankalin yan najeriya game da sirrin wayar da ta bayyana tsakanin Dan takar shugaban kasa Peter Obi da wani bisho.

“A wayar wanda ta bayyana ya kawo rudani tsakanin yan Najeriya yayin da akaji maganar Obi akan bisho yayi magana da kiristoci Kuma ya nuna musu cewa su zabe shi dan abun ya dawo yakin addini, bayan rudanin da ya kawo, ya Kuma fito yace wayar karya ce, an hada ne.

“In har wayar karyace, Toh ya fito ya nuna ta inda ta zama karya Kuma ya nuna yanda akayi ta zama karya tunda yayi wayar da bisho. Obi yakamata ya fito ya fayyace koh anyi wayar koh ba ayi bama gaba daya, koh kuwa hadawa akayi.

DOWNLOAD ZIP

“In hadawa akayi, ya nuna inda aka hada a jikin wayar, ta farko ne? Koh ta tsakiya? Koh ta inda yake fadin kalmar Yes daddy Koh ta inda yake fadin cewa yakin addini ne?”

Mohammed ya ce ita bayyanar wayar ta nuna cewa Obi yafito ne da kudirin yin siyasa ta addini da qabilanci.

Daily trust ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button