FootballLabaran Yau

Dan Wasan Kungiyar Kwallon Chelsea Ya Tafi Jinya

Dan Wasan Kungiyar Kwallon Chelsea Ya Tafi Jinya

Dan wasan gaba na kasar Belgium Romelu Lukaku ba zai buga wasanni biyu na gaba ba a gasar Nations league, bayan wani rauni da ya samu a agararsa, mai horar da ‘yan wasan Roberto Martinez ya fada a ranar Talata.

Lukaku ya ji ciwon ne a karawar da suka yi da Netherland kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

A ranar Laraba Belgium za ta kara da Poland sannan ranar Asabar ta kara da Wales, amma dan wasan na Chelsea ba zai buga duka wasannin ba in ji Martinez.

Belgium ta sha kaye a hannun Netherland a karawar da ci 4-1 a Brussels.

DOWNLOAD ZIP

Sai dai Martinez ya ce raunin “bai yi muni ba” kamar yadda aka yi fargaba a baya.

“Akwai matukar wuya, idan zai buga wasanmu na karshe.” Martinez ya ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button