Labaran YauNEWS

Mun Aika Wasu Yen Bindiga Barzahu

Mun Aika Wasu Yen Bindiga Barzahu

Jirgin yakin saman sojin Nijeriya ya kashe wasu ‘yan ta’adda 34 a kauyen Mangoro da ke kan iyaka tsakanin jihohin Kaduna da Neja.

Majiyar rundunar sojin ta ce rundunar sojin ta Operation Thunder Strike, ta samu rahoton sirri da ke cewa, anga kimanin ‘yan ta’adda 70 a kan babura 40, da kuma wasu da ke tafiya a kafa, sun nufi hanyar Akilibu – Sarkin Pawa, kusa da kauyen Mangoro.

Ya ce, Yayin da jirgin ya nufo wurin, an ga ‘yan ta’adda da dama suna guje-guje don tsira da rayukansu, suna barin baburansu da fakewa a cikin dazuzzukan.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Jirgin NAF yayi ta ruwan bama-bamai akan yan ta’addan, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsu da jikkata wasu da dama.

Wata majiya daga makusanta kauyen Mangoro sun bayyana cewa an ga babura 17 da gawarwaki 34 da kuma bindigun ‘yan ta’adda 14”.

Sai dai majiyar bata tabbatar da ko ‘yan ta’addan da aka kashe su ne ke da alhakin kai harin kwanan nan a kan titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button