Labaran YauNEWS

Sojojin Da Suka Rasa Ransu A Hatsarin Jirgin Sama Ta NAF- Kaduna

Sojojin Da Suka Rasa Ransu A Hatsarin Jirgin Sama Ta NAF- Kaduna

Jirgin horas da jami’an sojojin saman Nijeriya (NAF) ya gamu da hatsarin da yammacin ranar Talata a jihar Kaduna, inda ake fargabar matukan Jirgin biyu sun mutu a wannan hatsarin. 

Majiyar ya shaida cewar Jirgin ‘Super Mushak’, wanda Jirgin ne na koyar da jami’ai ya yi hatsari a Kaduna din ne a lokacin da ake koyar da jami’ai a cikinsa.

DOWNLOAD MP3

A cewar majiyar Jirgin ya gamu da hatsarin ne a cikin sansanin NAF da ke jihar Kaduna.

Daraktan sashin yada labarai da Hulda da jama’a na rundunar sojin sama, Air Cdre Edward Gabkwet, bai amsa wa manema labarai ba sa’ilin da ta bukaci ya tabbatar mata da batun hatsarin.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button