Karku Zabi Shugaba Wanda Ya Wuce Shekaru 60 Sittin, Saqon Tambuwal Ga Yen Nigeria.
Gomnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal Mai Shekaru 56 Yayi Kira Ta Musamman Ga Yen Nigeria Da Karsu Kuskura Su Zabi Shugaban Da Ya Wuce Shekaru Sittin.
Idan Bamu Mantaba Kwanakin Baya Gomna Aminu Waziri Tambuwal Ya Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takaran Shugabancin Nigeria A Karkashin Tutar Jamiyyar PDP.
Gomnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal Yayi Kiranne Awajen Wani Taro Wanda Da Kungiyar Daliban Yen Qasar Nigeria Ta (NANS) Ta Shirya Don Nuna Goyon Bayansu Wa Gomnan A Kudirinshi Na Tsayawa Takaran Shugabancin Kasan. Taron Wanda Kwamishinan Matasa Da Wasanni Ya Wakilci Gomnan, Gomnan Yayi Kira Ga Yen Nigeria Da Suzabi Lafiyayye Wanda Zai Iya Jagorantan Qasar Batare Da Laulayi Ba, Yenda Yayi Misali Da Shugaban Da Zai Iya Zuwa Cikin Qanqanin Lokaci Yakawo Tarin Sauye-Sauye A Kasar.
Mawallafi: Yousuf Uthman Danmadami