Labaran Yau

Sojojin Kasa Na Najeriya Sun Basu Kari Karfin Tun A Shekarar 2015 A Cewar..

Sojojin Kasa Na Najeriya sun basu kari karfin tun a shekarar 2015 a cewar Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Yace karfin sojojin Najeriya ta karu akai akai a mulkinsa, wanda yanzu ita ce na hudu a Afrika, da banbanci bayan ya sameta a na bakwai a 2015.

Buhari ya fada a bikin paretin kala na shekarar 2023 wanda sojin Najeriya tayi a garin Abuja ranan Alhamis.

Ya ce karfin sojin Najeriya yayi qasa a watan mayu shekarar 2015, an samu ci gaba a fannin aikin soja, wajen yaki da yan ta’adda, masu satar mai, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifi a kasar.

 

A bayanin shi Yace cigaba da aka samu a karkashin shi sun kama daga karin karfin soja, horaswa, kayan aiki, alawus, da Kuma ingantattun magunguna.

“Duk hakan yazo ne cikin kiyaye wa, ingancin aiki, da Kuma buduwar aikin soji.

“Ci gaba da aka samu a wannan wurare ya kawo cigaba na sojojin da kuma aikin su na dokan kasa.

“Karfin sojin Najeriya yayi kasa sosai Kamin watan mayu 2015”. Cewar sa.

A bayanin shi, shekara bakwai da ya gabata, karfin soji ya karu har ya zamo na hudu a afrika ba na bakwai yanda muka samu a shekarar 2015 ba.

“Kasafin kudade na sojin mu daga shekarar 2020 zuwa 2022 kawai ya kai da an siyo motoci masu tsayayya wa Duk wasu kananan bamamai. Tankoki da sauran motocin yaki da na shiga daji da sauransu, don a kara yawansu da wanda aka siya tsakanin 2017 zuwa 2022.

“Makamai dayawa an siyo wanda suka hada da bindiga kala kala, motan bindiga da sauransu wanda Suna Zube don aiki.

“Kayan aikin yasa karfin sojin Najeriya ya karu, da yawan horaswa” a bayanin sa.

Buhari yace sojin Najeriya sun gyara yanayin aikin su dan su fuskanci zahirin yanzu, yasa hakan ya taimaka wajen cimma yan ta’adda a arewa maso gabashin Najeriya.

Hakan ya kai ga kamen yan ta’adda, wasu kuma ajiye makaman yakin su.

Shugaban kasan ya ce nasaran sojin Najeriya ya kai da komawan yan gudun hijira zuwa wuraren zaman su na asali, bayan taimakon da sojin Najeriya suke badawa wajen kawo sauki na musifu a wasu kasashen.

Muna bunkasa sojin Najeriya, Kuma sojan sama na daga cikin manyan ayyukan da muka sa a gaba na sojojin kasa. Mun kirkiro hakan dan kauda Duk matsalan rashin zaman lafiya ne a kasar.

Munyi kokari mun inganta sojin Najeriya dan fiskantan duk wasu kalubale da zasu iya bayyana a gaba.

Sojoji dubu 60 aka dauka daga hawan mu karagar mulki a shekarar 2015. Banda wanda suka shigo ta NDA kaduna.

Mun Kara Albashi da alawus dan mu su samu kwarin gwiwan yin aiki yanda yakamata.

Sojojin dubu hamsin da suka mutu, Mun baiwa yaransu scholarship na karatu tun daga shekarar 2015 zuwa yau. Mun gyara muhallin sojin Najeriya.

Daily Nigeria ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button