Zamu tuntubi gwamnan jihohi Kamin cire tallafi
Majalisan tattalin Arzikin kasa tace lokacin cire tallafi na man fetur baiyi ba, amma Suna shirye Suna aiki don tuntubar gwamnonin jihohi da sauran jiga jigen.
Ministan kudi, kasafi da tsare tsare, dakta zainab Ahmad ta bayyana wa manema labarai bayan zaman da sukayi na Majalisan tattalin arzikin.
Maitaimakin Shugaban kasa, Farfesa Osinbajo ya jagoranci tattaunawar a fadar Shugaban kasa dake villa a Abuja ranan Alhamis.
Tace sun amince da kirkiro kwamiti mai fadi na bincike da aiki dan duba wajen gano lokacin da ya dace a cire tallafin mai.
A bayanin ministan, zasuyi la’akkari da lokutan da hanyoyin da zasu yi amfani dashi don baiwa talakawa tallafi da kuma inganta yawan man fetur a kasa baki daya.
“Eh, baramu cire tallafin yanzu ba, yana nufin baramu cire ba har sai Mun gama aikin mu.
“Kuma dai Muna da dokoki guda biyu wanda zai sa a cire tallafi a watan yuni na shekarar 2023.
“Kuma idan kwamitin dake aiki wanda ya kunshi kwamitin gwamnati Mai shigowa, su zasu bayyana ko cire tallafin a lokacin zai yiwu ko bare yiwu ba. In zai yiwu za a cire a watan yuni.
“Amma in lokacin za a kai gaba, dole Zamu dawo mu gyara dokar cire wa, dan ba’a yi tsare tsaren kasafin kudin kasa na shekarar ta wuce watan yuni ba.
“Dalilan mu kenan wanda yasa dole muyi tuntuba, Muna bukatar ra’ayin gwamnoni dan su bamu jami’un da zamuyi aiki dasu dan tsaida manufa guda wajen cire tallafin.
“Abu guda daya dake bayyane shine Amincewar kowa kan cire tallafin da sauri dan ba tsari bane wanda zai kaimu kuma baramu iya jimawa ciki ba, Kuma in lokaci yayi, a cire tallafin a take”.
Cikin jawabi kan zaman da akayi, Gwamnan jihar jigawa Abubakar Badaru ya bayyana cewa gwamnati ta dau rahoto kan ambaliya.
Ya ce kwamitin tayi nazari kan matsalolin dake jawo ambaliyan, asara da akayi da kuma dauki da gwamnati take kokarin kai musu.
Jihohi goma sha shida sun bada rahoton ambaliya saura jihohi ashirin ake jira su mika dan zama akai saboda samo maslaha akan ambaliyan a zaman Majalisan tattalin arzikin kasa.
Daily Nigeria ta rawaito