Shuka Bishiyoyi Babban Jigo Ne Ga Rayuwar Dan Adam
tsakiyar makon nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci gangamin dasa bishiyoyi da aka saba yi duk shekara a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, a wani bangare na fadada dashen itatuwa da kare su, lamarin da ke taka muhimmiyar rawa wajen kare muhalli, da kyautata iska, da dakile kwararar hamada, da cin gajiya daga tsirrai daga dukkanin fannoni.
Shekaru 10 ke nan a jere, shugaba Xi ke halartar wannan gangami na shuka bishiyoyi, matakin da masharhanta ke kallo a matsayin manuniya, ga kyakkyawan misalin al’adar Sinawa, ta wanzar da kiyaye tsirrai domin raya muhallin halittu baki daya.
Wani abun lura a nan shi ne, baya ga kyautata muhalli da shuka bishiyoyi ke haifarwa, a al’adar Sinawa, mutane masu basira na yin kamanceceniya da bishiyoyi a bangarori da dama. Ga misali, Sinawa kan ce, “raya bishiyoyi da kuma mutum na daukar lokaci, amma idan an yi su da kyau, za a ci gajiya maras iyaka.”
A mahangar jagororin kasar Sin, kamar yadda shuka bishiyoyi ke da fa’idar gaske ga rayuwar dan adam, haka ma mutane masu basira ke da muhimmanci wajen gina kasa, da wanzar da manufofinta na farfadowa.
A nan, muna iya ganin kama tsakanin shuka itatuwa, da ci gaban da bil adama ke samu ta hanyar raya fasahohi, da ilimi, musamman kasancewar sassan biyu na daukar lokaci, amma daga baya su haifar da alfanu maras iyaka.
Masana al’amuran yau da kullum sun sha bayyana gamsuwa, da yadda fannin raya ilimi, musamman na kimiyya da fasaha, da sanin makamar aiki a wannan zamani, ke zamewa kasashe daban daban wata dama ta samun ci gaban ginin al’umma, sama da zallan albarkatu da wata kasa ke mallaka.
Har kullum, kasar Sin na zama wani muhimmin misali, na al’ummar da take samarwa kanta damar kyautata kwarewa a fannin raya muhalli da ilimi a lokaci guda, kuma sakamakon hakan ke baiwa Sinawa karin damammaki, na cimma manyan burikansu na rayuwa yadda ya kamata.