Labaran Yau

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Gwamnatin Tarayya Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu na Shirin Bitar Albashin Ma’aikata – Inji Akpabio
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya baiwa ma’aikatan Najeriya tabbacin shirin gwamnati na sake duba albashin ma’aikatanta a wani mataki na dakile illar cire tallafin man fetur din da gwamnatin tayi.

Shugaban majalisar dattawan, ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Ekiti, Abiodun Oyebanji, da ‘yan majalisar dokokin jihar daga jihar. Akpabio ya kuma lura da wahalhalun da cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Bola Ahmed

Tinubu ta y iya kawo wa jamaar kasa.
Cire tallafin kuma yana da alaka da hanyar da gwamnatin ta bi domin magance matsalar cin hanci da rashawa a bangaren man fetur, Akpabio yakara da cewa cire tallafin man fetur ne mafarin yaki da cin hanci da rashawa a tsarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button