Labaran Yau

Gwamnatin Najeriya Suna Kashe Naira Miliyan Daya Wa Kowani Dan Fursuna Cewar..

Gwamnatin Najeriya Suna kashe Naira Miliyan daya wa dan fursuna cewar minista

Gwamnatin tarayya tace Tana kashe naira miliyan daya kan kowani dan fursuna a shekara, wanda ake ciyar da su cikin gidajen yari na kasar gaba daya.

Sola Fasure, Mai bada shawara kan shafin sadarwa wa ministan cikin gida, Rauf Aregebesola, ya bayyana hakan a jawabin sa ranar Asabar, a Abuja.

A bayanin, ministan ya bayyana a wajen kaddamar dakin gado Ashirin na masu cutar covid 19, a gidan yarin Portharcourt.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Shi ministan ya ce aikin aiki wanda ya nuna jajircewa wajen inganta rayuwar yan fursuna, da Kuma jin kai na yan fursuna da ma’aikatan su.

Aregbesola ya kara da cewa Shugaban kasa Muhammadu buhari yayi kokari wajen magance yaduwar cututtuka cikin gidan fursuna.

“Ita dakin an gina ta ne domin cututtuka irin su tarin fuka da sauransu. Muna murna dan Shugaban buhari ya kawo Kuma ya zama abin nuna wa a tarin mulkinsa.

“Ba wai Muna da asibiti bane ko dakin magani ba kawai, yan fursunan suna samun kula na lafiyarsu fiye da jami’an” in ji shi.

Ministan yayi kukan kalubale da gidan fursuna ke fuskanta na rashin kula da kuma rashin sabonta gidan da kuma kyautata wa yan fursuna.

Ya bada tabbacin Gwamnatin tarayya ta kawo mafita wanda zai amfani gidan shekaru masu yawa.

“Wannan gidan fursuna Mai daukan mutum 1800 amma ya na cike da mutum 3067, wannan shine matsalar gidan fursuna a mafi yawan birane.

“Ma’aikatan ma Suna samun kalubale amma Muna ta kawo hanyoyin da zai kawo sauki wa gidan na lokaci Mai tsawo.

“Daga cikin sauqin shine gina gidajen fursuna mai daukan mutum dubu uku a shiya guda shida na fadin Najeriya. Na kudu maso kudu Tana Bori wadda take ku sa da jihar Rivers.

“Na Arewa maso yamma tana janguza a jihar Kano, Arewa ta tsakiya kuma a garin karshi Abuja wanda an kammalasu. Zamu kaddamar dana kano cikin kwanakin nan Kamin mu sauka a gwamnatin.

“Kuma a yanzu Ana aiki akan sauran wanda yanzu aikin ya kai abin nuna wa.

“Inaso in kuma jaddada cewa gwamnati zata daina ciyar da wanda suka karya dokan kasa, Yace Kuma su sanya kudaden abincin yan fursuna cikin lissafin kudaden da ake bawa Hukumar” a cewar sa.

Aregbesola ya takai ta da bayan cewa da yayi asibitin zatayi maganin rashin lafiyar yan fursuna da kuma jami’an fursuna.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button