Labaran YauNEWS

Lokaci Yayi Da Yakamata Buhari Ya Sauka A Kujerar Mulki- Dattijan Arewa

Lokaci Yayi Da Yakamata Buhari Ya Sauka A Kujerar Mulki- Dattijan Arewa

Kungiyar Dattawan Arewaacin Nijeriya (NEF) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta yin murabus daga mukaminsa, sakamakon yadda ake ta kashe-kashe mutane a fadin kasar nan, musamman a arewacin kasar.

Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na Kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ne ya yi wannan kiran a ranar Talata.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta da amsoshi kan kalubalen tsaro da muke fuskanta. Ba za mu iya ci gaba da rayuwa a karkashin umarnin masu kashe mutane, masu garkuwa da mutane, masu fyade da kungiyoyin masu laifi iri-iri wadanda suka tauye mana hakkinmu na rayuwa cikin aminci.

“Tsarin kundin mulkinmu ya tanadi cewa shugabanni su yi murabus bisa kashin kansu idan suna da kalubale na wasu dalilai ko kuma suka nuna cewa ba za su iya shugabancin ba.

Yanzu lokaci ya yi da Shugaba Buhari zai yi la’akari da wannan zabin da idon basira, tunda shugabancinsa ya nuna rashin iya samar da tsaro a kan ‘yan Nijeriya. Don haka ba zamu iya ci gaba da rayuwa a karkashin wannan yanayi ba har sai 2023 da wa’adin Shugabancinsa zai kare,” in ji Baba-Ahmed.

Ya ce kungiyar ta bayar da wannan shawarar ne bayan la’akari da nauyin da ya rataya a wuyanta, ya kuma bayyana cewa yana fatan wasu daga cikin ‘yan Nijeriya za su cigaba da ba shugaba Buhari shawarar ya yi murabus.

Ya koka da cewa kashe-kashe da cin zarafi da ake yi wa al’ummomi a yanzu sun zama al’amuran yau da kullum na ‘yan Nijeriya, tafiya a halin yanzu tana da matukar hadari, kuma ko zama kayi a gidanka, baka tsira ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button