Mai Jagorantan Super Eagles Augustine Eguavoen Ya Dire Daga Matsayinsa Na Kocin Yan Kwallon Najeria
Shahararren kocin tawagar ƙwallon sawu ta Najeriya mai suna Augustine Eguavoen ya dire daga kujeransa na mai jagorancin yan wasanni sakamakon gagara kai ita tawagar Super Eagles gasar Kofin Duniya ta wanda zaayi a Qatar 2022.
Mun samu gamshashen dalili neh daga sanarwan da qungiyan Nigeria Football Federation (NFF) ta wallafa a shafinta ta na yadda zumunta kan cewa ta soke kwantaragin shekara biyu da rabi da ta bai wa shi mai jagorancin da tawagarsa nan take wanda shidin sanannen tsohon ɗan wasan ƙasar najeriya neh.
“Nan bada jimawa ba daa sanar da sabuwar tawagar masu horarwan bayan duba cikin tsanaki don ɗora Super Eagles kan tafarki da zimmar fuskantar ƙalubalan da ke gabanta,” a cewar sanarwar.
Sanarwar ta ambato Sakataren NFF Mohammed Sanusi na cewa “mun gode wa kociyoyin bisa aikin da suka yi wa ƙasa sannan muna yi musu fatan alheri a ayyukansu na gaba”.
DOMIN SAMUN LABARUN KWALLO ⇒ DANNA NAN