Labaran Yau

Emefiele Zai Bayyana Gaban Kotu Ranar Talata Bisa Zargin Mallakar..

Emefiele Zai Bayyana Gaban Kotu Ranar Talata Bisa Zargin Mallakar Makamai Ba Bisa Ka’ida Ba

A ranar Talata 25 ga watan Yuli ne hukumar kula da harkokin gwamnati za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN wato Godwin Emefiele a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas.

Kotun zata saurari karar da hukumar ta shigar da Emefiele dinne bisa zargin sa da mallakar manyan makamai ba bisa doka ba, wadda a cewar hukumar ya saba da doka da od ana kasa, kuma wannan laifi ne babba a matsayin s ana wanda ya rike babban mukami a kasar nan.

Kotun ta aika da sauraran karar zuwa ga lauyoyin da ke da hannu a lamarin kuma an tattaro cewa Joseph Daudu, babban lauyan Najeriya (SAN) ne zai jagoranci karar wanda ake kara yayin da Nicholas Oweibo zai zama alkalin alkalin kotun.

An tuhumi Emefiele da tuhume-tuhume biyu kan zargin mallakar bindigogi.
Jami`ian mu sun karbo mana labarin cewa, abun na farko, ana tuhumar Emefiele da mallakar bindiga mai lamba 1 (JOJEFF MAGNUM 8371) ba tare da lasisi ba, wanda ya sabawa sashe na 4 na dokar bindigogi, kuma ana hukunta shi a karkashin sashe na 27 (1b) na wannan doka.

Abu na biyu kuma, ana zargin tsohon gwamnan CBN din da mallakar harsashi har guda 123 (cartridges) ba tare da lasisi ba, wanda hakan ya sabawa sashe na 8 na dokar bindigogi kuma hukuncin da ya dace a karkashin sashe na 27 (1) (b) (il) na wannan doka.

Hukumar na neman kotun ta yanke masa duka hukuncin da ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button