Labaran YauNEWS

Anata Baje Koli A Kasuwannin Raguna A Manyan Biranen Nijeriya

Anata Baje Koli A Kasuwannin Raguna A Manyan Biranen Nijeriya

 

Farashin raguna kan kama ne  daga N160,000 zuwa N170,000, wadanda kuma ake shigo da su daga sauran kasashe makwabta Najeriya kuma, sukan kai kimanin N600,000 zuwa N700,000.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Galibi makwabtan Najeriya, Chadi, Mali, kamaru, Da Niger sun yi fice wajen shigo da dabbobin da ake layya da su cikin kasar.

Wadda tuni zuwa yanzu manyan kasuwannin da ake hada-hadar dabbobin layyaya a Najeriya suka yi cika makil da raguna da shanu.

Idan aski ya zo gaban goshi masu azancin magana kan ce ya fi zafi, ko ya ya farashin dabobin suke a wadannan kasuwanni?

Nuruddin Sadiq Adam mai sayar da raguna ne a kasuwar rago da ke Apo a Abuja, babban birnin Najeriya, inda ya ce duk da cewa kasuwar sabuwa ce, mutane kan shigo don sayan raguna kuma farashin na kamawa daga N170,000, 160,000, wadanda ake shigo da su daga sauran kasashe kuma sukan kai kimanin N600,000 zuwa N700,000.

Shi ma Isyaka Muhammad dake sayar da raguna ya ce, kasancewar bana babu kudi a hannun mutane farashin dabbobin da sauki.

Ana shi bangaren, Isiyaku Umar da ke sayar da shanu da kuma raguna ya ce, farashin shanu a kasuwar kan kama daga N310,000, N500,000, N600,000 har na N700,000.

Ya kara da cewa babban kalubalen da suke fuskanta a kasuwar shi ne rashin hanya da za’a shiga cikin kasuwar, yana mai cewa da zarar an yi ruwa sai hanyar ta chabe.

A nasa bangaren Alhaji Idris dogo daka saida abincin dabbobi a kasuwar, ya ce mutane kan zo don sayan abincin rago daga sassa da dama na babban birnin tarayya Abuja.

Saurari hirar Hauwa Umar da masu sayar da dabbobi a kasuwar ta Apo

Read more ~ Labaranyau.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button