Matasa A Jihar Taraba Sun Shirya Karbar Siyasar Jihar
Matashin Dan Takara Daga Jamiyyar PRP Mai Neman Kujeran Majalisar Jiha Don Wakiltar Alummar Garin Zing Jihar Taraba, Hon Kasimu Haruna Ya Jaddada Shirin Matasa Na Karban Ragamar Mulki A Jihar Ta Taraba.
Hon Kasimu Haruna:
Kaman yenda kafada a baya sunana kasimu Haruna, haifaffen garin Monkin dake karamar hukumar Zing a jihar Taraba. Nayi Primary School na a Alheri Nursery and Primary School, Monkin na kammala 2006, na jona secondary na a Genaral Hassan Usman Katsina Unity College Bauchi na kammala 2011, nadawo gida na fara paputukan Neman halal Wanda da ikon Allah na jona FCE, Yola a 2014 nagama 2017.
Nadawo nacigaba da Neman halal tare da temako a GDSS, Monkin nakoyar tsawon shekaru biyu, atai kace dai a yanzun nayi employing na ma aikata a masana’anta na mutane sunkai mutane 7. Sunan ma’aikatan BBK TELECOMMUNICATION CENTER.
Hon Kasimu Haruna ya tabbatar da goyon bayan da matasa ke bawa takarar tashi da 2023 lokacin Matasa ne a siyasan jihar ta Taraba, Bisa Bawa tsoffi dayawa dama ba tare da ta6uka wani abun azo agani wa alummarsu ba.