Labaran Yau

Yadda Ake Hada Kunun Alkama (Kunu Meh Matukar Amfani)

Yadda Ake Hada Kunun Alkama A Saukake

Ita kunun Alkama yana da matukar amfani musamman ga masu ciwon shuga da hawan jini.
Mutanen da shekarun su ya fi ja, su suke amfani da alkama dan yana taimaka wa masu wannan matsala, amma dai Duk da hakan kowa ma na iya amfani dashi, abun ra’ayi ne.

Abubuwan Hadawa

1. Alkama Gwangwani Biyu
2. Gyada Markadadde A Kalla Rabin gwangwani
3. Kayan kamshi kamar su citta da kanamfari
4. Suga Kadan yadda zai miki
5. Nono kofi daya

DOWNLOAD ZIP/MP3

Yadda Ake Hadawa

1. Da farko za ki kawo garin alkama da wanda ba’a nika ba sai ki wanke alkamarki ki sa a tukunya ki dora a wuta.

2. Sai ki dauko gyadarki ki dama ki tace ki ajiye a gefe, sai ki duba idan ya yi sai ki sauke ki juye. Sannan ki dora ruwan gyada a wuta.

3. Idan ya tafasa sai ki dauko dafeffen alkamarki ki zuba ki barshi ya kara nuna.

4. Sai ki dama garin alkamarki kadan ki sa kayan kamshi.

5. Idan ya yi sai ki sauke ki zuba damammen garinki ki juya sosai.

6. Idan ya yi sai ki zuba suga da nono ki juya sosai ki sawa mai gida da yara.

Ana kuma iya dama garin alkaman kadan a Kofi da ruwan sanyi sai a tafasa ruwa a zuba a Kai yayi kauri asa Madara da sugar asha

THE END!!

Koyi yanda akeyin wasu girke girken daga bisani ⇓

1. Yadda Ake Gwaten Dankali (Irish Potato Pottage)

2. Yadda Ake Gwaten Doya (Yam Porridge)

3. Yadda Ake Alale (Moi Moi)

4. Yadda Ake kosan Rogo

5. Yadda Ake Yar Tsame

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button