Sojojin Najeriya Sun Bayyana Kamfanin Bindiga A Taraba
Babban ofishin tsaro na kasa tace sojojin operation whirl stroke sun shiga kampanin kera bindiga a garin wukari na jihar Taraba Kuma sun kama mutum biyu wanda ake zargin masu safaran bindigogi ne.
Daraktan sadarwa na ofishin tsaro, Musa Danmadami, ya bayyana hakan ranan Asabar, yace sojijin sunyi aiki ne da sirrin fasaha.
Danmadami Yace, sojin Najeriya ranan jumma’a sun samu bindigogi kamar haka, GPMG guda biyu, KPM guda daya, AK47 guda hudu, pistol guda uku, PKT guda daya, 9mm guda biyar, 7.63 x 54 harsashi guda biyu.
Gindin bindiga guda bakwai da sauran jikin bindigogi daban daban a wajen.
Ya ce wanda aka kama, da bindigogi da harsasai an mika su zuwa ga Hukumar da yakamata dan daukan hukunci akan su.
“Hukumar sojin ta yaba wa sojojin Kuma Tana kara musu karfin gwiwan yin aikinsu. Ta bada shawara wa jama’a dasu yi amfani da sojojin dan magance wata matsala ta ta’addanci Kuma su bada bayani mai inganci kan Duk wani abinda zai kawo tashin tashina” a cewar sa
Daily Nigeria ta rawaito