Kocin Arsenal, Mikel Arteta, ya ce kungiyarsa za ta bukaci daukan point 114 don lashe gasar Premier League a gaban Manchester City. Yace yin unbeaten din shine kadai clean hanyar da Arsenal ke dashi dan zarce Man City.
A kakar 2022/2023, ‘yan wasan Pep Guardiola sun ci nasara da tazarar maki biyar. Amma a 2023/2024, Arsenal ta rage ta zuwa biyu. Arteta ya ce yanzu kungiyarsa za ta bukaci kamala da karin nutsuwa don samun damar doke zakarun.
Yace wannan ba abun mamaki bane daga kungiyar shi in aka duba rawar da suka taka a kakar baya da na bayan baya. Arsenal ta kare a matsayi na biyu a bayan Man City a kaka biyun da suka wuce.
Kungiyar Arsenal tayi saye saye masu tasiri a baya wanda ya hada da tsoffin ‘yan wasan Man City, Gabriel Jesus da Zinchenko.
Sannan zuwan Declan Rice, babban attacking Midfielder dake tashe a wannan lokaci a farashi mai matukan yawa. ‘Yan wasa kamar su Saka, Martinelli, Gabriel Jesus sun kasance zafafan strikers dake iya daga wa ko wani irin defence hankali.
Sauran teams kamar su Man United, Chelsea, Liverpool, da Tottenham basu da chance din kawo wa team din Arsenal wani tirjiya a tseren gasar.
Arteta yace a kakar daya gabata sunyi gida da waje wa Man U, sake yin hakan ba abu ne me wahala wa ‘yan wasan sa ba duk da ma Man U nata kokarin gyara baya da gabanta.
Kalaman Mikel Arteta Kocin Arsenal Dalla Dalla
Lokacin da aka tambayi kocin Arsenal abin da zai yi don doke City zuwa nasara, Mikel Arteta yace:
“Maki 114. Idan muka yi haka, za mu ci nasara tabbas.
“Wannan ita ce manufar, daga nan za mu ga abin da muka samu. Sami haƙƙin cin nasara kuma ku sami babban yuwuwar akan abokin gaba.
“Lokacin da muke da matsaloli cewa har yanzu mun fi abokan hamayya. Wannan shi ne ainihin manufar.”