Arsenal 3 – 1 Man United
Declan Rice da Gabriel Jesus sun ci kwallo a karshen wasa wadda ya basu narasa akan Man United ranan Sunday.
An kusa tashi a wasa, Rice da Jesus suka chanja wasan. A farkon wasa Marcus Rashford yasa kwallo wa Man United, amma Martin Odegaard ya rama cin a cikin sakanni 35 bayan an cisu.
Wasan abun kallo ne, saboda Man United sunyi tunanin sunci wasan a minti 88 lokacinda Garnacho yayi free da gola yaci, amma VAR ya kashe cin saboda Garnacho yana offside. Erik ten Hag yayi bakin cikin hakan.
Maimakon haka kuma, Declan Rice wadda Arsenal suka saya £105m yaci kwallo, inda yasamu kwallon da aka bugo kona a sama, ya riketa da kyau kafin ya buga kwallo da karfi duk da golan Man United yayi kokarin hanata shiga, amma ta bugi hanun sa sannan ta shiga raga.
Evans ya nuna cewa akwai foul, amma lokacin yayi nisa a murnan sa nacin wannan babban kwallo.
A lokacinda Man United suketa kokari dan hanin sun rama kwallon, Gabriel Jesus kuma ya rufe wasan, inda ya sallami Dalot a kasa sannan yaci kwallon sa a nitse.
A first half, Odegaard ya kusa cin kwallo amma sai kwallon ta bugi gefen raga a sakanni 35 da fara wasa.
Arsenal sun aza sun samu daman cin kwallo a minti 60, lokacin da alkalin wasa ya bada penalty, amma bayan bincike me kyau da VAR yayi, an kashe cin bayan an gano Wan Bissaka bai yi foul ba, Kai Havertz ne yake neman hakan.
Karshen wasan yayi wa Arsenal dadi saboda sun tafi da point 3, kuma sunci wasa guda 3 a cikin wasa 4 da suka buga, wadda yasa yanzu sune na 5 a table na Premier League.
Man United suna na 11 a table, kuma har yanzu basu ci wasa ko daya a Away ba.
Click To Check Out Arsenal Vs Man U Full Highlights Here