Labaran Yau

YANZU YANZU: Jirgin Sojojin Sama Yayi Hadari A Jihar…

YANZU YANZU: Jirgin Sojojin Sama Yayi Hadari A Jihar Benue

Wani jirgin saman horar da sojojin saman Najeriya FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

Sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Juma’a a wani atisaye na yau da kullum.

Gabkwet ya ce matukan jirgin guda biyu sun tsira kuma ana lura da su a wani wurin soji. Ya ce:

“An yi sa’a, matukan jirgin biyu da ke cikin jirgin sun tsira daga hatsarin bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin. Bugu da kari, babu asarar rayuka ko asarar dukiyoyi a kusa da yankin da abin ya shafa.

“A yanzu haka duka matukan jirgin biyu suna karkashin kulawa a asibitin NAF Base Hospital, Makurdi. A halin da ake ciki, babban hafsan hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin hatsarin nan take da kuma nesa.”

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button