Labaran Yau

Yan Bindiga Dadi Sun Harbe Mutum Biyar A Plateau

Kimanin mutane biyar ne ‘yan bindiga suka kashe a kauyen Nchya na gundumar Mangu a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.

Shaidun gani da ido sun shaidawa jami’in mu cewa an kashe mutanen kauyen ne da misalin karfe 1:00 na safe.

Da yake magana da manema labarai, wani ganau, Joshua Musa ya ce al’ummar yankin sun kwashe gawarwakin a cikin motar daukar kaya zuwa garin Mangu.

DOWNLOAD MP3

Kashe mutanen da akayi, wanda basu ji ba basu gani ba yayi sanadiyyar zanga-zanga a garin Mangu.

Wutar Da ‘Yan ta’addan Dajukan Zamfara Da Katsina Ke Karba Hannun Sojoji Ta Tilasta Masu Neman Sulhu

Alamu masu karfi na nuni cewa karin hare-hare ta sama da rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji a yankin Arewa maso yammacin Najeriya ke yi a ‘yan kwanakin nan na iya tilastawa jagororin ‘yan ta’adda a jihohin Katsina da Zamfara yin tunanin barin makamansu domin shiga fagen tattaunawa da gwamnatin tarayya.

Sakamakon yadda aman wutar ta hargitsa su, an yi imanin matakin na nuni da wani abu na tsoro da firgita daga bangaren ‘yan ta’addan da suka yi zargin cewa hare-haren bama-bamai ta jiragen sama na ci gaba da kai wa rayuwarsu da gidajensu da dabbobinsu hari.

DOWNLOAD ZIP

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button