Labaran Yau

Buhari Yasamu Nasara Kan Tsaro A Shekara Takwas Cewar Fadar Shugaban Kasa

Buhari yasamu Nasara kan tsaro a shekara takwas cewar fadar Shugaban kasa

Fadar Shugaban kasan Najeriya sun bayyana nasaran da akasamu a harkar tsaro tsakanin shakarar 2015 zuwa 2023.

Mai bada shawara wa Shugaban kasa kan shafin sadarwa, Femi Adesina, ya bayyana a takarda mai peji 90 ranan lahadi a Abuja, cewa an kawo canje canje kan tsarin jami’an tsaro.

Yace an zabi Buhari ne a jam’iyyar APC bayan kada Shugaban kasa mai ci a wannan lokaci na jam’iyyar PDP Goodluck Jonathan.

An rantsar dashi ranan 29 ga watan mayu 2015, a jawabin shi bayan rantsuwa ya ce zasu kula da Tattalin arziki, suyi yaki da rashin gaskiya da bin doka Kuma su kawo tsaro.

Wannan abubuwa guda uku yasa a gaba Kuma su yake kallo, tun daga shekarar 2015 a mulkinsa.

Adesina ya nuna ginin Hukumar imigireshan an kammalu tun shekarar 2016 Kuma da wasu ofishin su na wasu jihohi 17 da Kuma wasu da akeyi yanzu a Rivers, Bauchi, kogi da Ondo.

Hakan ya kawo cigaba yayin da Shugaban kasa ya amince da hadakai da bin tsari na MIDAS, don magance matsoli tsaro na bisa, da kuma yin aiki da yan sandan kasa kasa dan cimma burin tsaro a filin jirage na sama.

Fadar Shugaban kasa sun ce ita hukumar immigration sun gina dakin takanolaji a shekarar 2021 wanda zata saka ido Kuma ta kula da lamarin.

Hakan yasa ake kula da shiga da fitan mutane ta na’urar yan gizo. Hakan yasa ake aiki da kasashe dayawa dan samun bayanai masu amfani.

A shekarar 2021 zuwa 2022 yan drugs sun kama masu halkalla miyagun kwayoyi, da kuma diloli 29.

Fadan Shugaban kasan sun ce Hukumar ta kulle sama da 3,400.

Adesina ya bayyana cewa sun kama ton 5500 wanda kama kilo miliyan biyar da rabi na miyagun kwaya.

Shi Adesina ya bayyana Shugaban kasa Muhammadu Buhari da bawai dagun kafa yan gidan yari guda 2600 a kasa gaba daya dan gyara na Hukumar hukuncin masu laifi.

Wanda sun kai kashi uku da digo biyar cikin dari na yan yari, mafi yawansu wanda suka dare shekara 60 a duniya. Kuma wanda basu da lafiya koh wanda tsufa yayi yawa.

Sai Kuma masu laifin yin kwanan yarin shakara uku zasuyi wata shida.

“Masu rashin lafiyan kwakwalwa da wanda zasu biya dubu hamsin, da wanda aka ajiyesu ba a musu hukunci ba da wanda basu da laifi Duk acikin wanda aka sake” a cewar sa.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button