Labaran Yau

SHAWARA!! Kar Kaje Kanata Zukan Magani Ka Karyawa Yar Mutane Wheel Balance – Jamila Ibrahim

Shahararriyar meh bada shawara na kafar Fezbuk meh suna Jamila Ibrahim ta saki sabuwar bidiyo tana bawa mazajen aure shawari kan yanda zasu zauna da matansu kuma su tafiyar da zaman auren ba tareda an samu matsala ba.

Jami’inmu na Labaranyau Blog ya kawo muku cikakken shawarin da Jamila Ibrahim ta bayar bayan ta bada shawari wa mata akan yanda xasu tafiyar da zaman aure ga cikakken bayani dan kasa kadan ⇓

Bari mu dawo kan maza tunda jiya akan mata nayi magana

Wasu na complain cewa matansu basuda kokari malalata ne , Basu da kokari wajan oza room activities…

Malam kabar matarka da aikin gidan kaman ya ka*sheta , ga Yara kusan bakwai itace Yi masu wanka , gyaran gida , dafa abinci ga wankin Yara har da naka ma …

Sannan Kila tana Yan kana Nan sana’a a gida , Babu wata yar aiki , sai ta wuni a gajiye Dan ganin komai ya kankama …

Dan Rashin adalci kaje waje ka shawo maganin baban Aisha , Vega da wasu jike jike Duk ka tsuma kuma baka riko mata Koda Dan tsire da yoghurt ta Dan Sami kwarin jiki ba ka diran mata kaman zakayi yaki yaushe zata iya daukan ka 😕

Yanda jikinta yayi tsami da ayyukan gida Duk yanda take son faranta Maka bazai yiwu ba , sai dai tayi maneji tayi Daya ta buge da bacci …

Idan kasan bazaka rage mata aikin gida ka dinga bata abubuwan Sa kuzari ba kaje ka Kara aure …

Kar kaje Kanata zukan magani kazo ka karyawa yar mutane wheel balance 😴

A dinga sassautawa don Allah, Auren Nan ba wajan judo bane , atoh a dare Daya dai bazaka gama dashi ba , matar ka na Nan tare da Kai …

Idan Babu kanta yau gobe ma rana ce 🚶🚶🚶🚶

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button