Ana zargin Yan Ta’adda da kashe sarkin gunduma, Ardon birni da kewayen Zazzau Shuaibu Muhammad da yaran sa guda hudu.
Al’amarin ya faru ne cikin daren Asabar, da karfe 10 a Dorayi na karamar hukumar zaria a jihar Kaduna.
Yan ta’addan sun kai mutum biyar sun sace shanu guda dari na mutanen da suka kashe.
Matar mamacin, Malama Halima Shuaibu ta fadawa manema labarai bayan janazar wanda suka mutu, cewa an harbe mijinta a kai.
“An fitar da Ardo daga dakinshi aka harbe shi a kai sau biyu, nan ta ke ya mutu.
“Yan bindigan sun shiga daki daki a gidan suka kashe min yara hudu wanda dukan su ma’aurata ne Suna da yara.
“Wanda aka kashe akwai Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da Ibrahim Haruna.
“Bayan harin da sukayi a gidan, sun fita da shanu dari” cewar ta.
Wanda ya rayu bayan hari cikin yaran Ardo, Abdulrahman Shuaibu ya ce bayan sun kashe mutum biyu yayin da yan ta’addan suke fita daga kauyen.
Mai magana da yawun yan sanda na jiha, DSP Mohammed Jalige, Yace har yanzu ba kawo musu rahoton harin ba.