Labaran Yau

Sama Da Mutum 4,387 Suka Rasu A Hadarurruka Cikin Wata 6, Sanadiyar Hanyoyin Marasa Inganci

Sama Da Mutum 4387 Suka Rasu A Hadarurruka Cikin Wata 6 Sanadiyar Hanyoyin Marasa Inganci

Akalla mutane 4,387 ne suka mutu a hadarurruka a fadin kasar nan daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 30 ga watan Yuni na shekarar 2023.

Wani bincike mai zaman kansa da wakilan mu suka hado daga hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ya nuna cewa a rubu’in farko na shekarar mutane 1,080 ne suka mutu a hadarurruka 2,056 da aka samu.

Daga cikin mutane 13,415 da suka rasu a hadarurrukan hanyar, 6,803 sun samu raunuka yayin da aka ceto mutane 5,879 ba tare da jikkata ba.

Sai dai a rubu’i na biyu na shekarar, adadin hadurran ya haura zuwa 2,635 yayin da mutanen da suka yi hatsarin mota ya karu zuwa 16,354, inda aka ceto 8,919 ba tare da jikkata ba.

Haka kuma adadin wadanda suka mutu ya karu inda 3,307 suka rasa rayukansu yayin da 7,305 suka samu raunuka.

Alkaluman da hukumar ta FRSC ta samu sun nuna cewa, babban birnin tarayya Abuja ce ta fi kowacce yawan mace-mace inda adadin ya kai 615 yayin da jihar Bayelsa ta samu mafi karancin wadanda suka mutu inda takwas kacal a cikin wannan lokaci.

Ya ce, “Mun yi imanin cewa aikin kiyaye hanyoyin ya shafi kowa da kowa. FRSC ba za ta iya yi ita kadai ba. Hakki ne na gamayya shi ya sa muke tsayawa mu zama masu ruwa da tsaki a ko’ina kan hanyoyin kasar nan.

Hukumar tayi kira ga jamaa da su dinga kiyaye dokokin hanya sannan su dinga la`akari da kyawun abin hawar su kafin su hau hanya da su.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button