Labaran Yau

YANZU-YANZU: Kotu Ta Bada Belin Emefiele Kan Naira Miliyan 20

YANZU-YANZU: Kotu Ta Bada Belin Emefiele Kan Naira Miliyan 20

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta bayar da belin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da aka dakatar a kan kudi N20m tare da mutum daya da zai tsaya masa.

Mai shari’a Nicholas Oweibo ya kuma bayar da umarnin a tsare shugaban bankin da aka dakatar a gidan yari na Ikoyi, har sai an kammala belinsa.

Mai shari’a Nicholas Oweibo ya bayar da belin Emefiele bayan ya saurari shawarwarin lauyan Emefiele, Joseph Daudu (SAN).

Dazu dazunnan muka kawo maku labarin cewa Gwamnan babban bankin kasa CBN, Godwin Emefiele da aka dakatar ya isa babbar kotun tarayya domin gurfanar da shi a gaban kuliya bisa tuhumar sa da laifuka biyu da suka hada da mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba.

Alkalin ya yi watsi da ikirarin gwamnatin tarayya na cewa Emefiele na da hatsari.
Ya yanke hukuncin cewa gwamnati ta gaza bayar da wasu hujjoji da za su tabbatar da ikirarinta.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a matsayin shugaban bankin koli a ranar 9 ga watan Yunin 2023. Kwana daya bayan haka, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da cewa shugaban babban bankin na CBN da aka dakatar da shi yana hannun ta.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button