Labaran Yau

Sai Kun Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cewar Tinubu Wa Hafsoshin Sojin Kasa

Sai Kun Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cewar Tinubu Wa Hafsoshin Sojin Kasa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cewa wa hafsoshin tsaro na kasa kan dole su kawo maslaha na karshe dan samun zaman lafiya da tsaro na kasa dan kare lafiya da dukiyar yan kasa.

Mai bada shawaran tsaro na kasa, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana wa Yan jarida a gidan gwamnati cewa shugaban kasa ya zauna da hafsoshin tsaro da inspeto janar na yan sanda, a Fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.

Shugaban kasa ya amince da zaben su na mukaman su a watan Yuni ran 19 ga shekarar 2023.

Tinubu

Maganar sa bayan zaman ya bayyana cewa shugaban kasa ya nemi hadin kai wajen aiki tsakanin hukumomin a matsayin Kungiya daya dan samun aiki Mai inganci.

Tsohon shugaban EFCC ya bayyana zimma da cika aiki a dabi’unsu, yace za ayi aiki in shaa Allah.

Yace hafsoshin zasuyi aiki ba hutu ba dan a samu tsaro ba, har zaman lafiya za su kawo.

Akan zaman dasu kayi, Ya ce “Muna nan ne dan muyi godiya wa shugaban kasa dan bamu mukamai muyi aiki wa kasa. Muna Kuma mika wuya gareshi da Najeriya da yan Najeriya. Mun yarda da zabin shi Kuma shine mafi kyau. Kuma Mun san Mai yake so wa kasan.

“Zamu aiki ba gajiya dan yin aiki tukuru dan cimma bukatun mu na samar da tsaro, zaman lafiya, dan mu dawo da rayuwar mu yanda take dan cigaban mu.

“Ya bamu karfin gwiwa da goyon baya dari bisa dari, yace mana Kuma Sai munyi aiki kai a hade Kuma Musan cewa akwai aiki sosai a gaban mu. Kuma yana so mucika aiki, shi yasa muke nan”.

Zaman ta hada da Shugaban Ma’aikatan tsaro Major Janar Christopher Musa, Shugaban Ma’aikatan sojojin kasa Major Janar Taoreed Lagbaja, Shugaban Ma’aikatan sojin ruwa Rear Admrl Emmanuel Ogalla, Shugaban Ma’aikatan sojin sama Air Vice Marshal Hassan Abubakar, Chief of Defense Intelligence Major Janar E.P.A Undiandeye, mai rikon kwaryar inspeto janar na yan sanda Kayode Egbetokun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button