Labaran YauNEWS

Takara 2023- Ziyarar Amaechi Wajen Sarakunan Kano

Takara 2023- Ziyarar Amaechi Wajen Sarakunan Kano

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ziyarci Sarkin Kano da na Bichi a yayin da ya fara tuntunba da neman shawara kan tsayawarshi takarar Shugabancin Kasa, kwanaki kadan da shelanta sha’awarshi na tsayawa takarar.

Ya ziyarci Sarakunan ne a fadarsu da ke Kano da Bichi, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya tarbe shi hannu bibbiyu, inda ya ya bawa Ministan da ya zabi jihar Kano a matsayin jiha ta farko da zai ziyarta bayan ayyana takararshi.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Na san Amaechi tun yana kakakin majalisa, zuwa lokacin da ya zama gwamna, gashi yanzu ya na minista, wadannan matakan kadai sun isa gareshi ya samu cancantar takarar shugabancin kasa.” inji Sarkin Kano.

A nashi bangaren Sarkin Bichi, ya bayyana alakarshi da Amaechin, sannan ya mishi fatan alheri shi da sauran ‘yan takara. Sannan ya bukaci ‘yan takarar da su tabbata sun fifita Nijeriya fiye da kawukansu. Ministan ya mika godiyarshi ga Sarakunan kan kalaman girmama game da karfafawa da fata na gari da suka mishi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button