Yadda Ake Hada Tuwon Amala
Ita wannan tuwo ta samo asali ne daga kabilar yarbawa (Yoruba), ita ce tuwon da aka sansu mafi galibi masu ci Dayawa. Duk da dai a yau mutane daga kabilu daban daban sun koyi ci Kuma Suna ci sosai ko lokacin da ta kama.
Abubuwan Hadawa
Garin bawon doya kofi biyu
Garin alabo( garin rogo) kofi 1
Ruwa
Tukunya
Muciya
Yadda Ake Hadawa
Ki tankade kofi daya na garin bawon doyan daban a wani kwano. Ki dauko garin alabonki kofi daya da garin bawon doyanki kofi daya sai ki hada su gu daya ki tankade a wani kwano daban.
Ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa daidai yanda tuwonki ba zai yi ruwa ruwa ba kuma bawai ya yi tauri ba ki rufe tukunya nadan wani lokaci, sai ki dauko garin bawon doyan wanda ki ka tankade kofi daya da farko ki sa masa ruwa ki dama.
Idan ruwan ya tafasa sai kiyi rude ki rufe nadan wani lokaci sai ki dauko garin alabon ki wanda ki ka hadashi da garin bawon doyan ki tuka ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci kadan sai ki sauke ki sake tukawa ki kwashe a kula ko ki daure su a leda.
Ana cinshi da kowani irin miya.