Girke GirkeLabaran Yau

Yadda Ake Miyan Daddawa

FREE AIRTIME

Yadda Ake Miyan Daddawa

Kayan Hadi

Daddawan kalwa
Attaruhu
Tattasai
Albasa
Tafarnuwa
Citta
Manja
Maggie
Gishiri
Bushasshen kifi

Yadda Ake Hadawa

Dafarko za a samu daddawan kalwa Mai kyau sai a daka daddawan kadan kar yayi laushi, sai a bare kifin a wankeshi da ruwan dumi da gishiri, sai a daura a kan wuta a sa mishi ruwa Rabin cup a barshi ya silala idan ya silala sai a sauke asa a gefe

Sai a daura manja a soya shi da albasa,sai a wanke kayan miya a markada a zuba a cikin manjan a soya,a zuba dakkaken daddawan a yi ta soyawa har sai daddawan yayi kamshi sossai, sai a daka citta da tafarnuwa a ciki sai wannan kifin da a ka silala da Dan ruwan jikin kifin duka a ciki tare da Maggie da gishiri sai a Dan rage wutan,a barshi na tsawon minti talatin ya nuna a hankali miya ya kammala.

Ana cinsa da tuwon gero ko dawa ko da Duk wanda ya samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button