Yadda Ake Farfesun Kifi Cikin Karamin Lokaci
Hanya mafi sauki dan hada farfesun kifi muka kawo muku. In an bi sharudodin bara a ji kunya ba wajen dafa farfesun kifi Mai dandano.
Kayan Hadi
Kifi (tarwada)danye
Lemon tsami
Citta
Tafarnuwa
Masoro
Gyadan inyamurai
Attaruhu da albasa
Maggie
Gishiri
Za’a fara da wanke kifin da kyau ne saboda cire karni zaayi amfani da lemon tsami a goga dakyau ajikin kifin awanke dashi sai asa a tukunya
Sai a daka citta, tafarnuwa,masoro,gyadan inyamurai, attaruhu da albasa a zuba akan kifin asa Maggie da gishiri sai a zuba ruwa a daura a wuta a rufe tukunyar
Bayan wasu mintuna kamshin zai fara tashi alamun ya fara nuna sai a barshi yasake kaman minti biyu zuwa uku sai a sauke baa son ana jujjuyawa saboda zai farfashe.
Idan ma wani kifinne ba tarwada ba duk Hakan zaayi ferfesun
A ci dadi lafiya