Yadda Ake Miyan Ridi Cikin Karamin Lokaci
Kayan Hadi
Manja
Maggi
Gishiri
Kaza
Nikekken ridi
Tattasai
Attaruhu
Albasa
Ganyen ogu
Citta
Tafarnuwa
Daddawan inyamurai
Yadda Ake Hadawa
Za a sa nikkaken ridi a kwano a yayyafa mai ruwa sai a yita murzashi har sai ya fidda Mai kamar yadda ake fidda man agushi sai a ajiye a gefe , sai a dauki kaza a wanke a sa a tukunya a sa tafarnuwa,albasa, Maggie, citta gishiri a dafa shi dasu sai a ajiye shi a gefe
Sai a daura tukunya a sa maja a ciki a yi blichin din shi wato har sai yayi fari sai a sauke shi kasa ya huce , sai a markada kayan miyan tattasai, attaruhu da albasa kar yayai laushi sai a zuba a cikin manjan da ya huce a mayar kan wuta, sai a zuba daddawan inyamurai asoya su tare, idan ya soyu sai a zuba ruwan naman tare da naman,Maggie da gishiri idan ya tafaso sai a faffasa dunkulallen ridin da aka cire Mai a ciki sai a wanke ganyen ogu a yaka a zuba Shima ba a sa ganyan dayawa kadan ake sawa saboda ana so yayyi daddaya daddayane sai a juya a rufeshi
Sai a bashi minti ashirin ya dafu sannan sai a sauke.
Ana cin shine da tuwon shinkafa,semovita ko sakwara.