Girke GirkeLabaran Hausa

Yadda Ake Girka Miyan Rama

Miyan Rama wata miyane na abincin Hausawa wanda ake hadawa da tuwo, miyane wanda zaisa mijinki yaji dadinsa.

Idan har zakibi wannan salon hada miyan Raman toh lallai zaki mallake kan mijinki ba tareda shiga halaka ta hanyan wani sihiri ko tsubgu ba.

Jami’inmu na Labaranyau Blog ya kawo miki salonda da zakibi dalla dalla domin hada miyan rama wa angonki.

Tuwo Miyan Rama
Tuwo Miyan Rama

Abubuwan da ake bukata

1. Rama

2. Gyada

3. Attaruhu

4. Tattasai

5. Citta

6. Tafarnuwa

7. Maggi

8. Gishiri

Yanda ake hadawa

  • Dafarko zaki daura ruwan miyan a wuta sai ki jajjaga attaruhu da tattasai da albasa ki zuba ki daka gyada ki zuba kisa maggi da gishiri
  • Sai ki wanke raman ki tabbatar duk wani kasa ya fita sai ki zuba a ruwan miyan ki diga kanwa saboda ganyen yayi laushi ki rufe tukunyar abar komi ya dafu
  • Miyan Rama ta kammala

Ga bidiyon yanda ake hada miyan rama daga bisani ⇓

Yanda Ake Kwadon Rama

Zaki iya hada Kwadon Rama cikin minti kadan ba tareda kin kashe makuden kudiba

Abubuwan da ake bukata

1. Rama

2. Karago

3. Albasa

4. Attaruhu

5. Tumatur

6. Maggi

7. Gishiri

Yanda ake hadawa

  • Dafarko zaki wanke ramar tsaf ki tabbatar kin cire duk wani kasa da ke jiki sai ki daura a wuta kisa ruwa daidai ramar ki barshi yadafu tsawon minti 30
  • Sai ki juye a matsami zaki ciccire zare zaren jikin raman ki barshi ya tsantsame
  • Sai ki yayanka albasanki da tumatur
  • Ki daka karagon kisa maggi da gishiri sai kisa attaruhu ki pappasa akan karagon a juye a roba
  • Sai a juye ganyen a hada komi tare a jujjuya

Aci dadi lafiya.

Yadda Ake Sarrafa Kunun Gyada Mai Shinkafa, Ayaba, Da Sauran Yanayi Daban Daban

Yadda Ake Hada Miyar Taushe Wato Miyar Gyada Meh Dadi [Updated]

 

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button