Labaran YauLabaran Bauchi

Hukumar Yan Sandan Kasa Na Bauchi Ta Karbi Sakon Bada Kariya Da Neman Izinin Zanga Zangan 1 Ga Watan Augusta

Kungiyoyi masu lasisi da sauran al'umma sun sami izinin samun Kariya da izinin hanyoyin zanga zanga daga hukumar yan sanda na Kasa dake Bauchi state(Bauchi State Command)

Hukumar Yan Sandan Kasa Na Bauchi Ta Karbi Sakon Neman Bada Kariya Da Izinin Zanga Zangan 1 Ga Watan Augusta Zuwa 10 Ga Wata

A ranar 16 ga watan yuli ne kungiyar Northern Initiative for Growth ta jagoranci mika sakon neman kariya da izinin hanyoyin da za abi na zanga zangan da za’a fara 1 zuwa 10 ga watan agusta.

Shugaban rukunin Bauchi state commad ya karbi sakon ne bisa ga ka’idodin da doka ta shardanta na irin wannan yanayi.

Kungiyar sunyi dalla dalla da manufansu dakuma hurumi da doka ta kaiyade suna dashi na yin zanga zangan kwanciyar hankali.

Karawa da zaana wa shugaban rukunin Bauchi state command da kuma hukumar yan sanda ta kasa(Nigerian Polic Force)baki daya hanyoyi da dabi’un da kungiyoyin zasu tabbatar mutanesu sun kiyaye akan manufan zanga zangar.

Cikin girmamawa kungiyar ta zayyana bukatun ta na neman cikakkiyar kariya na hukumar yansanda don samun daman aiwatar da zanga zangar cikin kwanciyar hankali kamar yanda manufa tazo da ita.

Hanyoyin da sakon ta zayyana sun kasance na kwaryar cikin garin bauchi ne, wanda ya kunshi hanyar gidan gomnati, na gidan sarki da sauransu.

Zanga zangar zata fara ne daga fillin kwallon unguwar kobi wanda shine wurin taruwa ta farko kafin tafiya ta fara a ranar 1 ga watan agusta. Sai a bi ta titin kobi wato wanda aka fi sani da(Kobi street).

Kungiyar tayi nuni da cewa daga titin kobi za mike ta kasuwar wunti a bi Ahmadu bello way wanda zata zaga ta bullo hanyar gidan gomnati.

Daga gidan gomnati, zanga zanga zata bi manyan hanyoyi zuwa gidan sarki wanda daga nan kuma za a wuce a je matsaya.

Matsayar ta kasance kusan tsakiyar gari za ace, wato wurin babbar fillin kwallon kafa ta jiha, Abubakar Tafawa Balewa Stadium dake kusa da wunti market.

Daga karshe sakon ta kunshi jaddadi da tuni wa hukuma kan sanin sharadin dokan kasa da jama’a da kuma kungiyoyi sukayi domin jaddada wa hukumar yansanda.

Sannan sun nuna goyon baya dari bisa dari wa kungiyar hukumar yan sanda ta kasa wurin aminta da sharudan da hukumar zata bi don tabbatar da kare lafiya mutane gaba ki daya.

Wannan sakon yana nuni da manufar jama’a wurin ganin cikan burin yin zanga zangar cikin kwanciyar hankali da kuma lafiya.

HOTON SAKON NEMAN KARIYA DAGA KUNGIYA ZUWA GA HUKUMAR YAN SANDA A BAUCHI

Sakon Neman Izinin Zanga zangan Bauchi
Sakon Neman Izinin Zanga zangan Bauchi

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button