Labaran Yau

Jama`ar Nijar Sunyi Zanga-Zangar Nuna Goyon Baya Ga Juyin Mulki

Jama’ar kasar Nijar sun fito kwan su da kwarkwata domin nuna goyon bayan su ga juyin mulki da akayi a kasar sati biyu da suka gabata, jama`ar dai sun taru ne a wani dandalin da ke tsakiyar birnin Yamai, babban birnin Nijar.

A bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai, gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi kira ga jama’a da su fito domin yin tir da takunkumin da kungiyar Ecowas ta yammacin Afirka ta kakaba mata.

ECOWAS din dai ta bada wannan sanarwar ga jagoran juyin mulkin na kasar Nijar, sanarwar ta umurci sojojin da su mayar da mulkin kasar ga zababben shugaban kasar Bazoum, kudurin da sojojin suka ce baza su cika ba, ECOWAS din ta kara da cewa idan ba a maido da shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki ba amfani da karfin soja zai iya zama matsaya ta karshe akan lamarin.

Taro mai yawan gaske na samari sun fito a dandalin domin nuna amincewar su, sun nuna alama ta samun ‘yancin kai.

Rike a hannayen su akwai taken adawa da Faransanci da wasu tutocin Rasha kaɗan.

Duk da wannan nuna goyon baya ga mutanen da suka hambarar da shugaban kasar, jama’ar Nijar da dama na adawa da juyin mulkin.
Akwai ra’ayi cewa wani mataki ne na manyan sojoji da ke cikin tafiyar maye gurbin al`amuran kasar gaba daya..
Amma a yanzu yayin da suke neman hujjar kwace ikon, ana nuna kyama ga Faransawa.
Sauran makwabtan Nijar din da aka samu juyin mulki irin su Mali da Burkina Faso inda shugabannin juyin mulkin suka karfafa dangantaka da Rasha. Itama Nijar na shirin daukar wannan matakin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button