Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki Da Sauransu A Saukake
Jami’inmu Na Labaranyau Blog Ya Samo Cikakken Bayani Akan Wankan Janaba Daga Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam [Rahimahullah].
(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin Maiduguri na shekarar 2006 a cikin Suratut-Taubah aya ta 100)
“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu:
1. Akwai ‘Siffatul ijza’ (ta wadatar)
‘2. Siffatu kamal’ (ta kamala).
Daga bisani cikakken bayanin yadda ake wankan kenan guda biyu
Wankan Janaba a siffar sa ta kamala* shi ne:
Idan ka zo za ka yi ko za kiyi wanka da ruwa a gabanka farkon abin da za ka fara yi shi ne:
- Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku,
- Sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne,
- Idan ka wanke gabanka ma’ana ka yi tsarki kenan, to daga nan kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai
- Ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma
yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude
musammam gashin sa na ka, - Idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani
abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a
kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a kanka. - To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina.
- To idan ka yi wannan ne ka kammala,
- Abu na karshe shine sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro.
Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan Janaba
In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila ne haka za a yi in ma wanka ne na Biki haka
mace za ta yi, idan wankan Jumu’a ne ma haka za a yi, wankan Idi ma haka za ka yi, banbanci
kawai shi ne NIYYA.
Idan mutum zai yi siffa ta ‘Al ijza’* wadda ta wadatar ba sai ka yi al wala a cikin ta ba,
- Kana zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina,
in ma wani kududdufi ne ko rami ko “swimming pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla
niyyar ka kafin ka shiga, - Daga ka fito abin da za ka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da
kuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi kenan, kuma ya halatta ka yi sallah da wannan wankan,
Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.
Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka
kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fi ka cikar kamala, ya fi ka lada.
Kasancewar ba a yi alwala ba ciki, wannan ka’ida ce ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL
ASGAR) idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban
kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin a ce babban ma ya
tafi.”
Yanda Ake Wankan Janaba A Saukake