Yau lahadi daya daga cikin jami’in mu na Labaranyau ya samu tabbacin labarin wani dan takarar majalisan jahar Bauchi wanda ya kudiri zagawa lungu da sako da kanshi dan raba billboard posters.
Dan Takaran mai suna Hon Hamisu Nuru Jibrin ya fito bainan jamaa ya cire duk wata girman kai domin raba billboard posters da kansa a cikin garin Bauchi.
Wannan abu yabawa mutane mamaki yanda dan takaran ya cire duk wata girman kai da nuna isa ya gwada cewa shima dan adam ne kaman kowa.
Hotuna sunata zaga kafar yada zumunta na dan takarar yanda yake rabon billboard posters.
Dama ita mulki ana bukatan mutum neh meh tausayi, rashin girman kai ko nuna qyama ga talaka, duk wadannan ababe sun nuna a jikin Hon Hamisu yanda zaku iya kallon hotunan daga bisani.