Labaran Yau

Rushe Rushe: Haryanzu Banyi Da Na Sani Ba In Ji Gwamnan…

Rushe Rushe: Haryanzu Banyi Da Na Sani Ba In Ji Gwamnan Kano

Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida yace har yanzu bai yi da na sanin rushe wasu daga cikin gine gine da ya umurci a rushe daga farkon hawan sa zuwa yanzu.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano Aminu Ado B ayero a gidan gwamnatin jihar kano din lokacin bikin Sallah Babba da ake kammalawa yanzu.

abba ya ce “Mai martaba sarki yana da kyau masarautar kano ta san da cewa mun dauki hanyar rushe rushe ne domin dawo da wurare da ake sayar ko aka sayo ba bisa ka`ida ba kuma zamu tabbatar dukkanin irin wannan wurare mun karbo su baki daya domin jama`ar kano su amfana da su.
saboda haka babu da na sani a rushe gine gine da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sayar”

Gwamnan ya godewa mai martaba sarkin da ziyarar da ya kawo masa tare da godewa sauran hakimai da masarautar ta kano baki daya da ziyarar tasu wadda ita ce ta farko tun bayan da ya karbi mulki a watan da ya gabata.

Gwamnan ya bayyana abubuwa da ya cimma kamar su biyawa dalibai sama da 55,000 kudin jarrabawar gama sakandare ta kasa wato NECO wanda ya bayyana cewa adadin kudin ya kai kimanin Naira Biliyan N1.5b, Gyaran wuta ta kan tituna wato Street lights a turance da kuma dakile aika aikan masu kwacen wayoyi a kan hanyoyin jihar ta kano.

Sauran ayyukan na gwamnan wanda yayi bayanin su sun hadar da dawo da tantance dalibai da suka gama degree na farko da first class domin biya masu karatu a kasashen waje kyauta don karo karatu, biyan albashi lokacin da ya dace, biyan fensho na maaikata da kwashe Bola da datti a cikin jihar baki daya.

Gwamnan yayi kira ga mai martaba sarki da ya goyi bayan duk wasu tsare tsare da aikace aikace da gwamnatin ta sa keyi da kuma shirin aiwatar da su.

A nasa bangaren kuwa mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce wanna ziyara yayi ta ne domin taya sabon gwamnan murnar Babbar Sallah kuma ya bada tabbacin goyon baya da kuma shawarwarin sa a inda aka bukata daga wurinsa da kuma duk wani abu da ze saka jihar kano din ta ci gaba.

Sannan sarkin yayi kira ga jamaa su taimaka wa marasa karfi domin su iya rayuwa a lokacin da aka cire tallafin man fetur a kasar baki daya..

Ga Bidiyon Wasu Rushe Rushen Da AKayi A Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button