Yadda Ake Sallar Gawa Jinsin Namiji Ko Mace A Sauwake
Idan Allah ya dauki ran wani naka akan suturtashine sai ayi masa salla kafin a kaishi makabarta, yau anan shafinmu na Labaranyau Blog zamu bayyana yanda ake sallar gawa cikin sauki.
Dukkanin Malamai na Mazhabobi sunyi ittifaqi Bayan kayi alola to ga yanda zaka gudanar da ita sallan gawan ⇓
1. Kabbara ta Farko;
Idan yayi kabbara ta farko,za’a karanta suratul Fatiha da sura a sirrance.batare da addu’ar bude sallah ba
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ اﻟﺒﺨﺎﺭﻱ (3/ 158) ﻭﺃﺑﻮ ﺩاﻭﺩ (2، 68) ﻭاﻟﻨﺴﺎﺋﻲ (1/ 281) ﻭاﻟﺘﺮﻣﺬﻱ (2/ 142) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ ﻓﻲ ” اﻟﻤﻨﺘﻔﻰ ” (264) ﻭاﻟﺪاﺭﻗﻄﻨﻲ (191) ﻭاﻟﺤﺎﻛﻢ (1/ 358 – 386)
2. Sannan yayi kabbara ta biyu,sai yayi Salati ga Annabi Muhammad ﷺ , satul Ibrahimiyyah.
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ اﻟﺸﺎﻓﻌﻲ ﻓﻲ ” اﻻﻡ (1/ 239 – 240) ﻭﻣﻦ ﻃﺮﻳﻘﻪ اﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 39) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ (265) .
Wato shine:
« ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺻﻞِّ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ . ﺍﻟﻠﻬﻢَّ ﺑﺎﺭِﻙ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤَّﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﻣﺤﻤَّﺪ، ﻛﻤﺎ ﺑﺎﺭﻛﺖَ ﻋﻠﻰ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﺍﻫﻴﻢ؛ ﺇﻧَّﻚ ﺣﻤﻴﺪٌ ﻣﺠﻴﺪ »
3. Sannan sai kayi kabbara ta Ukku.
Bayan kabbara ta ukku kuma sai kayi addua ga mamacin ka kyautata yimasa addua da jumawa kana yin addua agareshi.
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺑﻮ ﺩاﻭﺩ (2/ 68) ﻭاﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ (1/ 456) ﻭاﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻓﻲ ” ﺻﺤﻴﺤﻪ ” ﻭ (754 – ﻣﻮاﺭﺩ) ﻭاﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 40) ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ ﻭﺻﺮﺡ اﺑﻦ اﺳﺤﺎﻕ ﺑﺎﻟﺘﺤﺪﻳﺚ ﻋﻨﺪ اﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ.
Ga misalin wasu daga cikin Adduar Manzon Allah ﷺ yayiwa mamaci-
-اﻟﻠﻬﻢ اﻏﻔﺮ ﻟﻪ ﻭاﺭﺣﻤﻪ، ﻭﻋﺎﻓﻪ ﻭاﻋﻒ ﻋﻨﻪ، ﻭﺃﻛﺮﻡ ﻧﺰﻟﻪ، ﻭﻭﺳﻊ ﻣﺪﺧﻠﻪ، ﻭاﻏﺴﻠﻪ ﺑﺎﻟﻤﺎء ﻭاﻟﺜﻠﺞ ﻭاﻟﺒﺮﺩ، ﻭﻧﻘﻪ ﻣﻦ اﻟﺨﻄﺎﻳﺎ ﻛﻤﺎ ﻧﻘﻴﺖ ﻛﻤﺎ ﻳﻨﻘﻲ اﻟﺜﻮﺏ اﻻﺑﻴﺾ ﻣﻦ اﻟﺪﻧﺲ، ﻭﺃﺑﺪﻟﻪ ﺩاﺭا ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺩاﺭﻩ، ﻭﺃﻫﻼ ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺃﻫﻠﻪ، ﻭﺯﻭﺟﺎ ﺧﻴﺮا ﻣﻦ ﺯﻭﺟﻪ، ﻭﺃﺩﺧﻠﻪ اﻟﺠﻨﺔ، ﻭﺃﻋﺬﻩ ﻣﻦ ﻋﺬاﺏ اﻟﻘﺒﺮ، ﻭﻣﻦ ﻋﺬاﺏ اﻟﻨﺎﺭ”
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ (3/ 59 – 60) ﻭاﻟﻨﺴﺎﺋﻲ (1/ 271) ﻭاﺑﻦ ﻣﺎﺟﻪ (1/ 4256) ﻭاﺑﻦ اﻟﺠﺎﺭﻭﺩ (264 – 265) ﻭاﻟﺒﻴﻬﻘﻲ (4/ 40) ﻭاﻟﻄﻴﺎﻟﺴﻲ (999) ﻭﺃﺣﻤﺪ (6/ 23 ﻭ 28) ﻭاﻟﺴﻴﺎﻕ ﻟﻤﺴﻠﻢ،
-اﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻪ ﻋﺒﺪﻙ ﻭاﺑﻦ ﻋﺒﺪﻙ ﻭاﺑﻦ ﺃﻣﺘﻚ:ﻛﺎﻥ ﻳﺸﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺃﻻ ﺃﻧﺖ، ﻭﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪا ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳﻮﻟﻚ، ﻭﺃﻧﺖ ﺃﻋﻠﻢ ﺑﻪ،اﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺤﺴﻨﺎ ﻓﺰﺩ ﻓﻲ ﺣﺴﻨﺎﺗﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﻣﺴﻴﺌﺎ ﻓﺘﺠﺎﻭﺯ ﻋﻦ ﺳﻴﺌﺎﺗﻪ، اﻟﻠﻬﻢ ﻻ ﺗﺤﺮﻣﻨﺎ ﺃﺟﺮﺓ، ﻭﻻ ﺗﻔﺘﻨﺎ ﺑﻌﺪﻩ “.
@ ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺎﻟﻚ (1 – 227) ﻭﻋﻨﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ اﻟﺤﺴﻦ (164 – 165)
4. Sannan kayi kabbara ta hudu,
A wannan kabbara ta huddun ne bayan kayi sai ka sakeyiwa mamaci addua ko kayiwa sauran muslmai addua.sannan kayi sallama.
Allah ne mafi sani.
Ga Bidiyon Yanda Ake Sallar Gawa A Saukake
MUHIMMIN TUNANTARWA
A Sallar gawa ana daga hannune kadai sau daya ne a cikin sallar gamawa, wato lokacin kabbarar Harama,sannan sai mutum ya dora hannunsa na dama akan na hagu abisa kirjinsa.
@Tirmizy da Darul Qadhny da Baihaqy
Mafi yawan mutane munayin asarar rashin sallar ga mamatan mu,yana da kyau a sami jama’a masu yawa sun sallace gawa saboda samun gafarar ga mamacin.
Annabi ﷺ yana cewa:
(Idan aka sami mutane arba’in wadanda basu shirka suka sallaci gawa suna neman citonaa awajan Allah,face Allah ya basu cetonsa).
@Duba littafin Ahkamul Jana’iz na Sheikhu Albany.
Allah ka bamu ikon yawaita yin sallah ga mamatan mu kuma kayi rahama da gafara a garesu baki daya.