Labaran Yau

Abinda Yasa Na Ziyarci Wole Soyinka – Peter Obi

Obi: Abinda yasa na ziyarci Wole Soyinka

Farfesa Soyinka ya bayyana cewa ma taimakin dan takarar jam’iyyar Labor Party Yusuf datti yayi maganganun da bai kamata ba.

Hakan yasa magoya bayan jam’iyyar suka saka farfesa a gaba da munanan kalamai.

Ya kara da cewa magoya bayan Obi Wanda aka fi sani da Obidient cewa hakan da sukeyi ya nuna cewa haka suke ba dan kasa ba.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Peter Obi ya manna hoton su tare da soyinka, a shafin Twitter, a inda ya bayyana cewa ya ziyarce shi ne dan samun fahimta kan abubuwan da suka faru.

Yace” Yau na ziyarci wani daga cikin masu girman daukaka a duniyar fasahan rubutu, wanda yasa a kasashen duniya, farfesa Wole Soyinka. Soyinka yana kamar uba guna wanda nake mutuntawa da martabawa kuma yana son cigaban Najeriya.

“Yana da tarihin yaki da rashin gaskiya kuma da rashin bawa kowa hakkinsa daidai, Kuma Baramu barshi ba.

“Mun samu ganawa da fahimta sosai da irin yadda yakeso Najeriya ta kasance, yadda za a bawa kowa yanci.

“Na tunatar ta shi farfesa ababen da yayi kamin yakin basasa da Kuma yanda yayi yaki wa mutan inyamurai.

“Naji dadin wannan ziyara da nayi ranan lahadi domin gyara alaka tsakanin mabiya dashi farfesa” a cewar shi.

 

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button