Labaran YauNEWSPolitics

Muna Sane Da Bata Garin Dake Niyar Fakewa Da Zanga Zanga Na 1 Ga Wata: Ministan Yada Labarai

A ranar Laraba 24 ga watan Yuli, ministan yada labarai, Muhammad Idris yayi tsokaci akan zanga zangar da ke zuwa a sabon wata.

Ministan yayi bayanin yanda me girma shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu ke jikkace da tunanin yanda wasu ke da niyar amfani da zanga zangar dan cinma mummunar nupin su.

Ministan yayi bayani sosai dan ganin yan kasa sun fahimci damuwan da shugaban kasa ke ciki dan tunanin lafiyan yan kasan sa.

Muhammad Idris a cikin bayanan sa ya kara da cewa shugaban kasa Tinubu yana tuni wa yan kasa da su san cewa yana sane da daman da dokan dimokradiyya ta bayar dan yin zanga zangar lumana. Sannan yana kari da cewa lallai idan har zanga zangar baza ta ratsa hakkin wasu yan kasan ba.

Ministan ya jaddada da yanda gwamnatin take jajircewa dan ganin ta kare hakkin yan kasa ta kowani hanya dakuma martabata.

Hakan yana nuni da gwamnatin na tare da dukkanin hakkin yan kasa a kowani hukunci ko ra’ayin da tayi, dakuma wanda zata yanke a gaba.

Ya kara nuni da cewa shugaban kasa Tinubu bayida wata adawa da zanga zaangar lumana da yan kasa ke shirye shirye yi.

Hasali ma sai dai muradin ganin an yi wannan zanga zaangar lumana a cikin lafiya da kwanciyar hankali. A wannan gaba ne rahoto tazo da cewa babban sufeta na yan sanda wato Kayode Egbetokun, yayi alkawarin nuna makura gurin bayarda kariya da kiyaye tashin hankali a ranar.

Amma ya jaddada da cewa matukar wannan zanga zangar bata kunshi rushe rushe da kone kone ba, suna nan da makurar kokarin su dan ganin sun bada kariyar.

Sannan zasu yi iya kokarinsu dan ganin sun tabbatar da zanga zangar ta kasance ta lumana kamar yanda dokar dimokradiyya ta wadatar.

Dukda cewa zanga zaangar tazo ne bisa da kunci da tsanani na wahalar rayuwa, ministan yayi alfahari da matasa gurin tabbatar da zanga zangar mai lumana ce.

Bidiyon Karin Bayani Akan Zanga Zanga Mai Zuwa

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button