Labaran YauTrending Updates

Tinubu Ya Roki Matasa Da Su Soke Shirye-Shiryen Zanga-Zangar, Ya Yi Alkawarin Kawo Mafita

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roki matasan Najeriya da su soke zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatinsa, yana mai tabbatar musu da cewa ya ji damuwarsu kuma yana iya bakin kokarinsa wajen magance su.

Ministan yada labarai Mohammed Idris yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa,  ya bayyana cewa Tinubu ya bukace shi da ya isar da sako ga matasa, inda yake basu hakuri akan su kara baiwa gwamnatinsa lokaci domin aiwatar da manufofinta.

Ministan ya bayyana saurin amincewa da kudurin dokar mafi karancin albashi da majalisar dokokin kasar ta yi a matsayin shaida na jajircewar shugaban kasar na magance kalubalen da kasar ke fuskanta.

Ya kuma bayyana amincewar da gwamnati ta yi na samar da isashen abinci kaman su hatsi da shinkafa ga gwamnatocin jihohi a wani bangare na kokarin dakile illar wahala ga ‘yan Najeriya.

Hatsi, Shinkafa Da Wake
Hatsi, Shinkafa Da Wake

Rokon da Tinubu yakeyi yazo a daidai lokacin da kungiyoyi daban-daban ke shirin gudanar da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatinsa, tare da nuna damuwa kan tattalin arziki, ilimi, da sauran batutuwa.

Ranar Lahadi wasu mutane cikin yankin Katsina sun nemi tada zanga zanga wanda har yanemi ya tada zaune tsaye tsakanin alumma.

Ga wata bidiyo wanda sukace daga bisani “An kai mu makura kan rashin tsaro a kauyukan Katsina in ji mutanen da suka yi zanga-zangar adawa da”

Ga bidiyon yadda zanga zangar tsadar rayuwa na NLC ta gudana a garin Abuja ⇓

 

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button